Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta soma fito da wannan tsarin na kakkafa rugage domin tsugunar da Fulani makiyaya, da zummar kauce wa yawace-yawacensu, wanda ake hasashen na zamowa musabbabin tashe-tashen hakula da kalubalen tsaro.
Sai dai yunkurin na gwamnatin tarayya ya hadu da kakkausan suka da rashin amincewa daga wasu sassan kasar, ciki kuwa har da shugabannin kungiyoyin Fulani da ake abin dominsu, lamarin da ya sa gwamnatin ta dakatar da shi.
Amma tuni wasu gwamnatocin jihohin Arewa, musamman masu fama da kalubalen tsaro, suka sha alwashin cigaba da wannan shirin, a zaman wani sashe na hanyoyin magance tashe-tashen hankali da ake ta’allakawa da Fulani ‘yan bindiga.
Jihar Zamfara, wacce ta dade tana fama da ayyukan na ‘yan bindiga, ta kasance ta farko wajen aiwatar da shirin, wanda gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya kaddamar a matsayin babban bako na musamman, a kauyen Ranji da ke cikin karamar hukumar mulki ta Maradun.
Gwamana Tambuwal ya kara da cewa wannan zai nuna kula ga irin rayuwar da makiyaya suke ciki wadda tana tattare da hatsari kuma da rashin kulawa inda aka fito, zai basu kwanciyar hankali na cewa gwamnatin ta maida hankali don inganta rayuwar su.
Mu’assasin aikin na ruga, gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, yayi bayanin dalilan da suka haifar da kafa rugagen na Fulani.
Matawalle ya ce aikin kafa rugagen Fulani na da manufar kyautata rayuwar al’ummar Fulani, makiyaya har ma da hausawa, ta yadda za su dace da wannan zamani da muke ciki.
Babban matsalar da muke ciki shine yawaitar munanan tashe-tashen hankula da ba’a taba ganin irinsa ba, wadanda aka gano cewa sun samo asali ne sakamakon rashin guraren kiwon dabbobi, da kuma hanyoyin dabbobin.
Da wannan, muke fatan wanzar da nasarar da muka samu ta dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara.
Su ma fulanin da suka halarci taron sun bayyana jin dadinsu da wannan shirin, kuma sun yi kira ga gwamanati da ta maida hankali wajen gina musu makarantu, hanyoyi da kuma asibitoci.
A karkashin shirin, za a samar da rugagen Fulani uku a jihar ta Zamfara, daya a kowace mazabar dan majalisar dattawa, inda kowacce za ta ci kudi naira miliyan dubu 2 da 800 (wato biliyan 2.8), kowacce kuma zata hada da giggina gidaje da samar da manyan hurumin kiwo, da makarantu da asibitoci da dai sauran abubuwan more rayuwa.
Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna daga Gusau:
Your browser doesn’t support HTML5