Matar shugaban kasar Nijar wadda ita ma likita ce tare da ministan kiwon lafiya suka kaddamar da shirin na tsawon mako daya a birnin Dosso.
Makasudin fadakarwar shi ne rage mace macen da da uwa domin haihuwan yara a jere babu wani lokaci da yakamata tsakaninsu yana yiwa iyaye da yaran da ake dora masu kanne tun basu gama rarrafe ba nada la'ani.
Malam Hassan Haruna jami'in asibitin sadarwar dake birnin Kwanni yayi karin bayani akan makon. Yace a kasashe masu tasowa talakawa na yawan mutuwa lokacin haihuwa. Wannan fadakarwar tana cikin kokarin da gwamnati keyi na taimakawa mata da zummar rage mace mace.
Yawan haihuwa akai akai kan kashe mahaifa saboda ba'a bata lokacin warkewa ba kafin wani cikin ya shigo. A cikin wannan yanayi yaron da aka hana shan nono sosai domin sabon ciki ya shigo shi akan rasa. Ana gargadin mata su yaye 'ya'yansu tukunna kafin su dauki wani cikin.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako.
Your browser doesn’t support HTML5