An Kaddamar Da Na'urar Gwajin COVID-19 a Najeriya

A Najeriya, an yi nasarar samar da wata na'urar da za ta taimaka wajen yaki da cutar coronavirus yayin da adadin masu kamuwa da ita ke karuwa a kasar.

A ci gaba da kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na yaki da cutar COVID-19 a kasar, an kaddamar da na'urar gwaji da za ta ba da sakamakon cutar nan take mai suna RNASwift wacce masana kimiya a kasar suka kirkiro suka kuma tabbatar da ingancinta.

A cewar mukkadashin babban shugaban hukumar kimiya da fasaha ta Najeriya NABDA Farfesa, Alex Akpa, wanda hukumarsa ta kirkiro da na'urar gwajin, ana sa ran wannan yunkuri zai taimaka wajen bunkasa hanyoyin gwada cutar COVID-19 da gwamnatin kasar ke yi.

Ya kuma bayyan irin ci gaba na karin basira a wuraren bincike da aka samu a kasar, tare da hadin gwiwar wasu masana kimiyya daga kasar Ingila.

Dan majalisar tarayya kuma shugaban kwamitin kiwon lafiya Yusuf Tanko Sununu, ya yaba da wannan ci gaba inda ya yi fatan ingancin sakamakon gwajin.

Sai dai ana shi bangaran Farfesa Abdulsalam Nasidi, Tsohon shugaban hukumar takaita cututtukka a Najeriya kana babban darekta da ke sa ido a cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kunyiyar Ecowas, ya ce, akwai sauran aiki a gaba.

A halin da ake ciki adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a kasar na kara yawa, inda adadin wadanda suka kamu ya haura 30,000, yayin da adadin wadanda suka warke ya haura dubu 12,000, an kuma rasa mutum sama da 600 a fadin kasar.

Saurari Karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Na'urar Gwajin COVID-19 a Najeriya