Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ke Haifar Da Matsalar 'Yan Shila a Adamawa?


Wani keke napep wanda 'yan shila ke amfani da shi a Adamawa
Wani keke napep wanda 'yan shila ke amfani da shi a Adamawa

Matsalar 'yan daba da ake yi wa lakabi da 'yan shila na cikin matsalolin tsaro dake addabar al’ummar jihar Adamawa inda sukan kwace wayar hannu, ko jaka da kuma yi wa mata fyade,

A wasu lokutan sukan raunata wanda suka kai wa hari dama kisa, kamar yadda ya ke yawan faruwa cikin kwanakin nan.

Bincike na nuni da cewa 'yan shilan akasarinsu matasa ne da basu wuce shekaru 14 zuwa 25 ba, kuma sukan fake da sunan suna sana’ar keke napep, ko kuma su boye a bakin hanya domin kwace dukiyoyin mutane.

Malama Sarah, wata mata ce wacce ita ma ta fada tarkonsu kuma ta bayyana wa VOA irin illar da suka yi mata.

"Ina zaune a gaban gida kawai sai na ga wani yaro ya fito daga keke napep, jim kadan kawai ya sare ni ta wuya na da kuma hannu na."

Wani wanda 'yan shila suka yi wa illa
Wani wanda 'yan shila suka yi wa illa

Yayin da wadannan mutanen ke addabar jama’a, ita ma, a nata bangaren, rundunar tsaron farin kaya ta sibil difens a jihar Adamawa ta bayyana cewa ta yunkuro don fuskantar lamarin, inda rundunar ta samu nasarar cafke wasu manyan 'yan Shilan.

Nuruddeen Abdullahi dake zama kwamandan rundunar ta sibil difens a jihar Adamawa ne ya tabbatar mana da hakan.

"A yanzu mun kama su kuma suna nan a gidan yari. Muna da tabbacin irin munanan abubuwan da suke aikatawa a gari."

Wasu dai sukan zargi iyaye da sakaci wajen bada kyakkyawar tarbiyya ga 'ya'yansu, wanda a cewarsu shi ke haifar da wannan matsalar. Wasu kuma sun alakanta irin wadannan lamuran da laifin gwamnati na rashin samarwa matasa aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG