An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da Suka Mutu

Nijar

Hukumomi a jihar Damagaram da ke jamhuriyar Nijar, sun gabatar da wata gidauniya don tallafawa iyalan sojojin da suka rasu a fagen daga, wanda hakan na iya zama hanyar karfafa hulda tsakanin jami'an tsaro da al'ummar gari.

Gwamnan jIhar Damagaram Musa Isa, ya ce hakan zai ba jami'an tsaro da mutanen gari damar yin aikin tabbatar da tsaro a cikin kasa, ya yin da su kuma al'umma za su kama hanyar taimaka ma hukumar yin aiki cikin sauki.

Assan Bagayya, babban jami'in ma'aikatar kwana-kwana wanda ya yi magana a madadin sojojin ya ce, sun ji dadin wannan tsarin, kuma zai tafi dai-dai idan har al'umma sun kama musu, ta hanyar ba su labari aduk lokacin da bukatar hakan ya taso. Hakan kuma na nuni da cewar ba su manta da 'yan uwan su sojoji da suka rasa ran su a fagen daga ba, da ma iyalan da suka bari.

Ya ce za su ci gaba da irin abubuwan nan don tallafa ma iyalan na su, inda su ma kungiyoyin farar hula suka yaba da tsarin, inji Mustafa Adam na kungiyar MPCR, wanda ya kara da cewar gwamnati ta kara fadada tallafin iyalan sojojin domin suna cikin tsananin bukata.

A saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da Suka Mutu