KANO, NIGERIA - Taron karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu halartar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, dan kasuwa Abdulsamad Isiyaka Rabiu da sauran su.
Gwamna Ganduje ya ce tashar za ta kara buda lamuran kasuwanci na jihohin arewa kasancewar tarihin cinikayya a Kano tun lokacin da a ke shigo da kaya da fatauci ta hanyar Sahara daga Afurka ta arewa da ta zama kofar shiga nahiyar turai.
A hirar shi da Muryar Amurka, babban manajan tashar Ahmad Rabiu ya ce za a yi gagarumin taro a Kano nan gaba kadan don fara aikin tashar kamar yanda a ka yi a Kaduna.
shi ma a nashi bayanin, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya nuna albarkar tashar za ta shafi duk yankunan cikin kasa da ba sa kan iyaka da teku, ya na mai addu’ar daurewar zaman lafiya.
Shugaban hukumar sufurin jiragen ruwa Emmanuel Jime ya sadaukar da nasarar kafa tashoshin kan tudun ga tsohon shugaban hukumar Hassan Bello wanda shi ne kwarerre da ke kula da aikin tashar ta Dala.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5