Firai minista Brigi Rafini ne ya fara karbar allurar a wannan kamfe yayin wani bikin da ya gudana a asibitin kwararru na Hospital General de Reference a birnin Yamai.
A cewarsa, allurar ita ce hanya mafi a’ala wajen kare kai daga kamuwa da wannan masifa.
Tuni aka ware wasu cibiyoyin na musamman a manyan biranen wannan kasa domin gudanar da ayyukan wannan kamfe wanda zai shafi wani rukuni na al’uma a zagayen farko kafin nan da mako 4 a sake yi masu wata allurar a zagaye na 2 in ji ministan kiwon lafiya Ahmed Boto.
Likitoci sun kara nanata gamsuwa da nau’in wannan allura da ta fito daga kasar China saboda a cewarsu ba wata tantama a game da kwarewar wadanda suka yi wannan aiki.
Wani jami’i a ma’aikatar lafiya ta kasa Zabeirou Souley ya karbi tasa allurar a wunin farko na wannan kamfe ya kuma bayyana mana dalilansa na shiga sahu.
A ranar Lahadin 21 ga watan Maris ne shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou mai shirin barin gado ya karbi rukunin farko na tallafin allurar riga- kafin cutar corona daga hannun jakadan kasar China wadanda aka kIyasta cewa ya kimanin 40,0000 ne da za a yi wa mutun 20,0000 kafin a nan gaba a samar da kari daga abokan hulda na waje.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5