Wannan yunkuri na tsige shugaba Hery Rajao-na-rimam-pia-nina ya samu goyon bayan ‘yan majalisu 121 daga cikin ‘yan majalisu 125 da suka kada kuri’unsu a yau laraba.
Yanzu ya rage ne kotun kundin tsarin mulkin kasar ta duba matsayar wannan kuri’a da aka kada, kafin a dauki mataki na gaba.
Shugaba Rajao-na-rimam-pia-nina, ya karbi mulkin kasar ne a watan Janairun bara, bayan komawa karkshin turbar dimokradiyya da kasar ta yi a shekarar 2006.
An sa ran, mulkin shugaban zai kawo karshen tarzomar siyasar da ta addabi kasar bayan da aka hambarar da gwamnatin Marc Ravalomanana a shekarar 2009.
Sai dai masu adawa da mulkin shugaban kasar na yanzu, sun yi ikrarin cewa gwamnatin ta gaza, kuma lokaci ya yi da za a kawar da ita.
A baya kasar Amurka ta nuna goyon bayan ta ga shugaba Ery, a shekarar da ta gabata ne kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta cire dukkanin shingayen baiwa kasar taimako, saboda nasarar zaben da aka yi, wanda ya samar da sabuwar gwamnati.