Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Manyan Jami’an Hukumar FIFA


U.S. Attorney General Loretta Lynch announces an indictment against nine FIFA officials and five corporate executives for racketeering, conspiracy and corruption at a news conference, in Brooklyn, New York, May 27, 2015.
U.S. Attorney General Loretta Lynch announces an indictment against nine FIFA officials and five corporate executives for racketeering, conspiracy and corruption at a news conference, in Brooklyn, New York, May 27, 2015.

Yau Larabar nan Amirka ta girgiza hukumar kwalon kafa ta duniya, FIFA, akan tuhumar jami'an hukumar na yanzu dana da, kan aikata laifuffukan zarmiya da cin hanci.

yayin da su kuma hukumomin kasar Switzerland suka bude nasu binciken akan zarge zargen da suke da alaka da yadda aka zabi kasashen da zasu karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas da shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu. An kam jami'n hukumar FIFA da dama a birnin Zurich.

Tuhumar da Amirka ke yi, sun hada harda zargin aikata laifuffuka arba'in da bakwai akan mutane goma sha hudu da suka hada da zamba da kokarin batar da sawun kudaden haram a makarkashiyar da lauyoyi suka ce sun danganci kudaden da shugabanin kafofin yada labaru suka bayar ko kuma suka yarda zasu bayar na cin hancin fiye da dala miliyan dari da hamsin.

Ma'aikatar shari;ar Amirka ta baiyana wannan makarkashiya ne ko kuma mataki da aka yi kimamin shekaru ashirin da hudu ana kulawa da nufin azurta kansu ta hanyar cin hanci da rashawa daya danganci wasan kwalon kafa na kasa da kasa.

Yau Laraba hukumomi a Zurich suka kama jami'an hukumar FIFA, kafin a iza keyar su uwa nan Amirka. Bugu da kari kuma hukumomin Amirka sun gabatar da iziin yin bincike a birnin Miami kuma ma'aikatar shri'ar Amirka tace tuni wasu mutane hudu suka amsa laifin cewa suna da hannu a wannan batu.

XS
SM
MD
LG