Ya jinjinawa abunda ya kira namijin kokari, sannan ya umurci askarawan su kara jan damara don kakkabe abinda ya kira burbushin ‘yan kungiyar daga wannan yanki, abun da tuni ya soma faranta ran jama’ar wannan yanki.
Ya kara da cewar, ddakarun sun gwadawa duniya cewa Boko Haram ba ta fi karfin a fatattake ba, haka kuma sun gwadawa mayakan wannan kungiya cewa ba da karfe aka haliccesu ba.
"Boko Haram ta shiga halin tagayyara, domin kuwa ta kidime ta rasa inda za ta shiga. Aikin dake gabanmu shine mu murkushe wannan kungiya saboda haka mu ci gaba da jajircewa don cimma wannan burin."
Yace wajibi ne su gwadawa Boko Haram cewa zasu ci gaba da yakar ta wur-janjan ba gajiyawa. Wannan ziyarar ta mataimakin hafsan hafsoshin Nijar a Diffa ta faranta ran mazauna yankin da ke bayyana cewa, ziyar tasa ta nuna cewar bai manta da dakarun tsaro na hadin gwiwar kasashen tafkin Chadi ba, idan akayi la’akari da nasarorin da yace ana samu a wannan yakin.
Masu sharhi a fannin tsaro na kallon wannan rangadi ga dakarun yaki a mtsayin cigaba da zai daure a cewar Kaftin Ali Yacouba mai ritaya.
Rahotannin karshen mako sun yi nuni da cewa wasu rokoki sun fadi a wani wurin dake da nisan kilomita 5 da garin Diffa, abinda wasu ke cewa filin jirgi ne aka auna amma haka ta kasa cimma ruwa.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5