An Jinjina Ma Dattijan Arewa, Amma Kuma

An bukaci da su ganar da shugaba Goodluck Jonathan muhimmancin samo hanyoyin sulhunta fitinun da suke faruwa a yankin arewacin kasar.
Masu sauraron Muryar Amurka da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan irin rawar da dattijan arewa suke takawa a yunkurin samar da zaman lafiya a wannan yanki na Najeriya, musamman ma a yankin arewa maso gabas inda aka fi fama da matsalar nan ta Boko Haram.

A cikin wannan kashi na ra'ayoyin da za a ji, masu sauraro irinsu Kasimu Aliyu Asadda Sokoto, Bashar Muhammad daga Abuja, Dr, Dayyabu badara daga Jihar Bauchi da Alhaji Lisko Bakaniken Mota More, duk sun yaba tare da jinjina ma dattawan na arewa, amma kuma sun bayyana ra'ayin cewa akwai baragurbi cikinsu, kuma tilas a yi tankade da rairaya.

Wasu su na ganin kamar shugaba Goodluck Jonathan bai jin maganar dattawan na arewa, wasu kuma su na kira a gare su da suyi amfani da tasirinsu wajen tabbatar da cewar shugaban ya gane muhimmancin yin sulhu maimakon daukar matakan soja kawai.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyin Jama'a Kan Rawar Da Dattawan Arewa Suke Takawa Kan Kawo Zaman Lafiya - 3:27