Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Dattawan Arewa Na Waswasin Alfanun Dokar Ta Baci


Wasu mata kenan ke kokarin kiyaye dokar ta baci
Wasu mata kenan ke kokarin kiyaye dokar ta baci

Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya da ke taro yau a Nijeriya sun nuna shakku kan fa'idar kafa dokar ta baci a jihohi uku na arewa maso gabashin Nijeriya.

Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya, da ke wani taro yau a Nijeriyar, ta nuna tababa kan ko shin kafa dokar ta baci da aka yi a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar na da fa'ida.

Da ya ke bayani ma Aliyu Mustafan Sakkwato na Muryar Amurka a yau dinnan, wani jigon kungiyar, Furfesa Ango Abdullahi ya ce ba gaskiya ba ne cewa kungiyarsu na tuhumar gwamnati da kin tuntubarsu kafin ta kafa dokar ta baci a jihohin Borno Adamawa da Yobe. Ya ce ai ba sai an tuntube su kafin a kafa dokar ba. Ya ce to amma su abin da su ke nuna rashin yadda da shi shi ne ana kan kokarin nemar hanyar warware takaddamar hukumomi da kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah Lid Daawati Wal Jihad (wadda ake wa lakabi da Boko Haram), kwatsam sai kawai aka kafa dokar ta bacin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG