An Jefi ‘Yan wasan Brazil Da Ayaba A Paris

Tawagar 'yan wasan Brazil

Baya ga ayabar, an kuma jefi 'yan wasan da gorar ruwa da wasu abubuwa.

An jefi ‘yan wasan kwallon kafar Brazil da ayaba yayin da suke murnar zura kwallo a wasan sada zumunta da suka buga da Tunisia a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Talata.

Dan wasan gaba na Brazil Richarlison da sauran abokanan wasansa suna murna bayan zura kwallo ta biyu a wasan da aka tashi da ci 5-1 sai aka jeho ayaba daga cikin ‘yan kallo a daidai kuryar filin wasan da suka taru suna murna.

Baya ga ayabar, an kuma jefi 'yan wasan da gorar ruwa da wasu abubuwa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Brazil ta yi amfani da wannan wasa na sada zumunta wajen dabbaka yaki da matsalar nuna wariyar launin fata, inda suka tsaya a gaban wani allo da aka rubuta; “da babu bakaken fata cikin ‘yan wasanmu, da babu taurari a rigunanmu – kalaman da ke nuni da taurari guda biyar da ke jikin tambarin kungiyar, wadanda ke nuna adadin kofin duniya da kasar ta lashe a baya.

Kungiyar kwallon kafar kasar ta Brazil ta yi Allah-wadai da wannan al’amari, tana mai nuni da cewa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen yaki da “matsalar nuna wariyar launin fata.”