An Harbi Wani Matashi a Lokacin da Suke Kokarin Kare Kuri'ar Mazabar su

  • Ibrahim Garba

Wani Sojan Najeriya

Wani soja dauke da makami

A yayin da ake gudanar da babban zaben kasa a Najeriya, rahotanni daga jahar Bauchi sun bayyana cewar an sami 'yar tangarda tsakanin wasu matasa da jami'an tsaro yayin da mutum guda ya rasa ransa. wakilin sashin Hausa Abdulwahab Mohammad yayi hira da wasu matasan da abin ya auku a kan idanun su.

Kamar yadda matashin ya bayyana, suna zaune a wani wurin da suke zaman dirshan wato jira da kuma tabbatar da kare kuri'un su daga magudin zabe a ranar Asabar da ta gabata sai jami'an tsaron 'yan sanda suka nemi korar su amma matashin ya ce, "mun hana 'yan sanda wucewa, hada motar su muka caje amma bamu ga komai ba sai muka barsu suka koma, ana haka ne sai kwatsam wata motar soji ta iso, Daf da tsayawar su sai wani daga cikin sojojin yayi harbi har ya hallaka daya daga cikin mu."

Matashin ya kara da cewa hatta wanda zai fadi sakamakon zaben saida muka tabbatar shi kadai ne kuma bashi dauke da komi, kuma munyi hakan ne saboda tabbatar da an aiwatar da gaskiya wajan kirga kuriun mu. Yayin da sojan ya bude wutar, ya harbi wani tsoho ya raunatashi sannan shi kuma dayan matashin ya rasu. Matasan sun kara da cewa a wurin suka kwana kuma jama'a da dama sun kaw masu taimakon abinci a yayin da suke zaman tsaron kuri'un.

A jahar Gombe kuma rahotanni sun nuna cewar an fitar sakamakon zaben daga yankunan kanannan hukumomi guda tara kuma ana kan tattarawa domin bada jimlar kuri'u da ko wace jam'iya ta samu domin gane wanda yayi nasara a zaben.

Rahotanni daga Bauchi da kuma gombe sun nuna cewar an sami gagarumar nasara akan mayakan nan da ake zaton 'yan kungiyar boko haram ne. A garin dukku kuma anyi artabu kuma an kashe na kashewa an kuma kama wasu da dama.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben 2015: An harbi wani matashi a lokcin da suke kokarin kare kuri'un mazabarsu - 3'43"