An Hana Zirga-Zirga Ranar Zabe A Plato

Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Yana Rangadin Runfunan Zabe

Rundunar ‘yan sandan jahar Pilato ta sanya dokar hana yawo a duk fadin jahar yayin gudanar da kammala zaben gwamna da za’a yi a rumfuna arba'in na kananan hukumomi tara na jahar Pilato.

Wata sanarwa dake da sanya hannun kakakin rundunar ‘yan sandan na jahar Pilato. DSP, Tyopev Terna, tace dokar hana zirga-zirgan zata fara aiki ne daga karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamman ranar Asabar.

Sanarwar tace daukan matakin ya zamo tilas saboda a ba jama’a dammar gudanar da zaben wanda suke so ba tare da wata musgunawa ba.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji

Your browser doesn’t support HTML5

An hana zirga zirga ranar zabe a Plato-2:00"