Kasar Pakistan ta hana wani jami’in diflomasiyyar Amurka fita daga kasar har sai an je kotu akan wani mummunan hadarin mota da ya shafi jami’in.
Hukumomi sun ce ranar 7 ga watan nan na Afrilun nan, babban jami’in tsaron ofishin jakadancin Amurka kanal Joseph Emanuel Hall ya tuka motar ofishin ya kuma yi karo da wani mai babur, har Attique Baig dan shekaru 22 ya mutu yayinda wani mutum kuma a kan keke ya raunana.
Mataimakin attorney Janar na Pakistan, Raja Khalid, ya sanar da kotu yau Talata cewa gwamnatin kasar ta sanya sunan Hall a cikin jerin sunayen masu manyan laifuka na kasar, an kuma hana shi fita daga kasar. Khalid ya kara da cewa an riga an sanar da duk tashoshin jiragen sama na kasar.
Iyalin mammacin ne suka kai kara a wata babbar kotu dake babban birnin kasar, suna neman a sanya sunan Hall a jerin sunayen wadanda ba za su iya fita daga Pakistan ba idan suna fuskantar irin wannan tuhumar.