Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Mutane 10: Yau Alek Minassian Zai Gurfana Gaban Koto A Toronto


Taswirar wurin da Alek ya kai hari
Taswirar wurin da Alek ya kai hari

‘Yan sandan kasar Canada na kokarin gano musabbabin wannan harin na jiya Litinin wanda ya kuma raunana mutane 15.

A yau Talata ake kyautata zaton wani Direban mota da ake zargi da kashe mutane 10 a lokacin da ya tuka wata babbar mota a ya bi ta kansu, a wani babban titi mai cunkuson jama’a dake birnin Toronto na kasar Canada, zai bayyana gaban kotu.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Toronto Mark Saunders ya bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Alek Minassian, dan shekaru 25 da haihuwa, ya kuma ce mazaunin wata unguwa ne a garin na Toronto. Saunders ya ce tabbas harin kamar dagangan aka yi shi.

Ministan kula da harkokin tsaron jama’a Ralph Goodale ya ce ya tuntube manyan jami’an tsaro kuma bisa ga bayyanan da aka samu “ana gani kamar batun tsaron kasa bai da alaka da lamarin da ya faru.” Wannan dai shine kisan mutane mafi muni a tarihin kasar Canada.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG