Mutane 7 sun hallaka a arewacin Nijeriya a wasu hare-hare biyu da ake zargin tsattsaurar kungiyar Islama ta Boko Haram da kai wa.
Shaidu sun ce wadanda su ka mutu din sun hada da ‘yan sanda 5 da fararen hula biyu ‘yan kallo.
‘Yan Boko Haram da dama ne dai su ka kaddamar da hari kan wani ofishin ‘yan sanda a garin Kankara da ke jihar Katsina da yammacin Litini. Daya harin kuma an kai ne kan wani banki a garin. To amman akwai rahotannin da ke cin karo da juna kan shin ko ‘yan Boko Haram ne su ka kai hari bankin ko kuma dai wasu ‘yan fashi da makami ne na yankin.
Kakakin hukumar ‘yan sanda ya ce ‘yan Boko Haram din ba su damu da kudin bankin ba.
Wannan kungiyar dai so ta ke a kafa tsattsaurar shari’ar Musulunci a fadin arewacin Nijeria. Ma’anar ‘Boko Haram’ da harshen Hausa dai shi ne ilimin boko haramun ne.
Kungiyar ta Boko Haram ta yi ikirarin kai harin bam kan hedikwatan ‘yan sanda a makon jiya a Abuja, babban birnin Nijeriya, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mutane.
A ‘yan shekarun nan an yi ta zargin kungiyar da kai munanan hare-hare a arewacin Nijeriya, da akan auna kan jami’an ‘yan sanda da jami’an gwamnati.