Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Ishiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.da labarin mutuwarta ya dauki hankalin ‘yan Najeriya da wadansu kasashen waje.
Bayan sauraran karar, Lauyan gwamnati kuma Mai shari’ah Muhammad Lawan ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairun wannan shekara domin ba lauyoyin gwamnati da aka zasu kare Abdulmalik damar gudanar da nasu binciken.
Kotun tana tuhumar mutanen uku da laifuka da suka hada da hada baki, garkuwa, boyewa da kuma ajiye wanda su ka yi garkuwa da da shi a wuri daya, da kuma kisan kai. laifuka da suka amsa aikatawa
Da yake tsokaci a kan batun, babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Musa Abdulahi ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa, za a yanke hukumcin a wannan shari’ar cikin watanni biyu babu makawa.
Tun farko, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ci alwashin aiwatar da hukumcin da kotu ta yanke da zarar an kai teburinsa.
Yace, ina so in tabbatar maku cewa, Ma’aikatar Shari’a za ta shigar da kara a kotun da ya kamata cikin kwanaki uku zuwa hudu masu zuwa. Zamu bi batun sau da kafa, kuma a cikin wata daya ko biyu masu zuwa za mu kamala maganar wannan karar.. Mu al’umma ce mai bin doka da oda.
Tun bullar labarin kashe Hanifa mutane ke bayyana fushinsu ta fannoni dabam daban. Bayan gano gawar Hanifa a harabar makarantar.
A daren jiya ne dai wasu matasan da ba’a San Ko suwaye ba suka cinna wa Makaranta Nobel Kids College da ke unguwar yan kaba kwanan dakata wuta , Makaranta da aka sace marigaya Hanifa Abubakar aka kuma kashe ta.
Tuni dai makwabta da motar kwana-kwana suka kashe gobarar- mun zanta da kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da faruwar hakan tare da cewar ba’a kai ga kama wadanda suka cinna wutar ba. Ya kuma yi Karin dangane da gurfanar da wadanda suka kashe Hanifa gaban kotu.
A halin da ake ciki kuma, ma’akatar ilimi ta jihar Kano ta dakatar da dukkanin makarantu masu zaman kansu dake jihar har zuwa lokacin da za a tantance su, biyo bayan garkuwa da kuma kashe Hanifa da mai makarantar da ta ke zuwa ya yi.
Da yake ganawa da manema labarai kan lamarin, kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru ya bayyana cewa, gwamnati za ta kafa kwamitin da ya kunshi masu ruwa da tsaki da zai tantance da kuma sake nazarin bada lasisi ga makarantun masu zaman kansu.
Ku Duba Wannan Ma Tsawon Kwanakin Da Aka Yi Garkuwa Da Hanifa Kafin Tuntubar Iyayenta