Wata kotun soja a Jamhuriyar Nijar ta fara sauraren shari’ar wasu dakarun kasar da ake zargi da yunkurin yin juyin mulki a shekarar 2015.
Kimanin kararraki 32 kotun ta fara saurara, amma uwa uba daga cikin kararrakin ita ce ta sojojin da suka yi yunkurin kifar da gwammnatin shugaba Isuhu a watan Disambar shekarar 2015.
‘Yan uwa da iyalan wadanda ake zargin ne suka halarci zaman wannan shari’a wanda aka yi a kotun da ake kira “Tribunale Militaire” da Faransanci.
“Muna fatan yau wannan abin da aka faro ya zamanto rana ce ta fitarsu insha Allah. Tun da abinda ake zarginsu da shi ba a samu wata hujja ba.” Inji daya daga cikin ‘yan uwan wadanda ake zargi.”
Gwamnatin Nijar ce ta shigar da karar domin ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Ministan cikin gida, Bazoum Mohamed, wanda ya wakilici ministan shari’a ya ce ya kamata mutane su amince da wannan kotu domin manyan hafsan sojojin na da kwarewa.
Sai dai, daya daga cikin lauyoyin da ke kare wadanda ake zargin, ya nemi da a yi gyaran fuska ga kotun hukunta laifukan soja ta yadda abin zai yi daidai da abin da ke akwai a kundin tsarin mulkin kasa.
Kundin tasarin mulkin Nijar ya nuna cewa dukkan ‘yan Nijar, soja da farar hula matsayin su daya a gaban doka.
An dai dage sauraren karar har sai ranar 23 ga watan nan na Janairu, bayan da lauyoyin wadanda ake zargi suka gabatar da wannan bukata.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5