Bincike ya nuna wurin da ake son kafa cibiyar tara iskar gas din, yana cikin rukunan mazaunin al’umma ne ba kamar yadda gwamnatin Jihar Bauchi ta tsara ba, da aka kebe wuri na musamman domin kamfanonin ya dangin wadannan.
Masu zanga zangar da ya hada har da maza da mata suna zargin mutumin dake son samar da matattarar Iskar gas din da yin watsi da umurnin da hukumomi suka bashi na tsaida aikin gina matattarar iskar gas din bisa la’akari da irin barazanar da zai iya faruwa. idan aka samu fashewa ko kuma gobara a wurin.
A dangane da wannan takardamar ne muryar Amurka ta tuntubi, kwamishina mai kula da muhalli na jihar Bauchi, Honorabul Hamisu Shira, inda ya shida cewa an kafa wannan wurin tara iskar gas bada sanin ma’aikatarsa ba, kuma baya kan ka'idar samar da irin wannan masana’antar a wurin da mutane ke da gidajen kwana.
Da murya amurka ta tuntubi mai Kamfanin Action Energy, Ahaji Nura Manu Soro ta wayar tarho, ya shaida cewa wurin na magada ne, abin da zai iya fada kenan akai.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5