Yamai, Niger - Taron, wanda ke matsayin wata haduwar shekara shekara, ya zo ne a wani lokacin da majalisar ministoci ta bada sanarwar shirin kafa ma’aikatar Agence Nationale de la Population, wacce za ta maida hankali wajen samo hanyoyin takaita yaduwar jama’a a kasar, da aka ayyana a jerin kasashen duniya mafi fama da dabi’ar tauye hakkokin mata. Dalili kenan batun ‘yancin mata ya dauki hankali a haduwar ta wannan karon.
Madame Miko Fatima Oumar, wadda ke daga cikin malaman da suka hau mambari, ta ce wannan aikinsu ne na fadakar da ‘yan uwansu mata.
A nan gaba ne Majalisar Dokokin kasar za ta nazarci wannan kudiri. Saboda haka malamai magada annabawa suka fara yunkurin tunatar da ‘yan majalissar nauyin da ya rataya a wuyansu.
Yawaitar mutuwar aure na daga cikin matsalolin dake cinye wa jama’ar Nijer tuwo a kwarya, inda bayanai ke nuna cewa abin na kara ta’azzara a kowace shekara, mafarin baje maudu’in hakkokin ma’aurata a kan teburin wannan haduwa. Limamin Masallacin Amir Sultan dake birnin Yamai, Check Mouhammad Sadis Abdourahaman, na daga cikin wadanda aka gayyato domin yin wannan tunatarwa. Ya ce akwai matsala tsakanin bambance kyautatawa da alhakki da yawancin lokuta ake dorawa kan addinin.
Aurar da yaran da ba su kosa ba da auren dole, matsaloli ne da hukumomi suka bayyana a matsayin abubuwan da suka hana Nijer samun ci gaba, yayin da yawan haihuwa ke zama cikas ga magidanta da ba su da halin daukar dawainiyar ‘yayan da suka haifa sakamakon tarin dalilai masu nasaba da matsanacin yanayin talaucin da kasar ke fama da shi, dalili kenan da mahukunta suka fara yunkurin yi wa tufkar hanci. Sai dai wasu ‘yan Nijer na ganin abin a matsayin wanda ya saba wa addini da al’ada.
Saurari rahoton Souleyman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5