WASHINGTON, D. C. - Hakan ya fito fili ne a yayin babban taron kungiyar ‘yan jihar ta Filato mazauna Amurka na wannan shekara.
A zahiri, mutane na kallon ‘yan kasashen Afirka da suka gidandance a manyan kasashen Turai da Amurka a matsayin wadanda suka manta gida domin sun taka ‘tudun mun tsira,’ musamman la’akari da dimbin kalubalen tattalin arziki da tsaro da suka baro a kasashen nasu.
To sai dai da yawa daga cikinsu, musamman ‘yan Najeriya daga jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar kasar, sun ce sam ba za su taba mantawa da gida ba, a cewar Dr. Barth Sheokong, shugaban kungiyar ‘yan jihar ta Filato.
Dr. Barth Sheokong ya ce “Gida ya dame mu, ka ga kamar kowane lokaci ina zuwa gida. Ina kokarin in je gida ko wane shekara. Ana cewa ‘idan ka bar gida gida ya bar ka’ to amma ba haka ba ne. Dukan mu muna da kishin kasar mu.”
‘Yan asalin jihar ta Filato da dama ne suke zaune a nan Amurka, wadanda kuma tuni suka kafa kungiyar tuntuba da taimakon juna har ma da gida.
Akasarinsu dai masana ne kuma kwararru a fannoni daban-daban na ci gaba, da kuma suke ayyuka iri daban-daban a nan Amurka, dalili ke nan da gwamnatin jiharsu ta asali ta Filato, ta ce akwai fa’idodi da dama da jama’ar jihar za su girba ta hanyar ‘yan uwansu da ke kasashen waje.
Barr. Caleb Mutfwang, gwamnan jihar ta Filato ya ce “Manufar zuwanmu nan shine mu zo mu kammala shirin yadda za mu amfana da irin ilmi da kwarewa da suke da shi. Shi ya sa ban aiki kowa ban an zo da kai na. Domin tun lokacin yakin neman zabe muka yi alkawarin cewa za mu kafa ofis na musamman domin sada zumunci da mutanen Filato da suke kasashen waje a duk duniya. Za mu ci gaba da daukar sunayensu da irin gwanintar da suke da shi don mu san yadda za mu ci moriyarsu.”
To sai dai gabanin aiwatar da wannan shiri, shugaban kungiyar ta ‘yan jihar Filato da ke Amurka, ya ce suna tallafawa al’ummar da suka baro gida ta fannoni da dama.
Dr. Barth Sheokong, ya ce “Maganar makarantu, asibitoci, wasu lokuta da ma irin abubuwan da ake samu na ‘crises’ da muke samu a gida, muna kokari mu ga yadda za mu taimaka wa wadanda rikicin na gida ya shafa.”
Daya daga cikin manyan kalubalen da jihar ta Filato ke fuskanta dai shi ne na tashe-tahen hankula da ake alakantawa da addini da kabilanci a ‘yan shekarun nan. A nan ma ma’ajin kungiyar Asabe Spencer-Mhya ta ce suna ba da gudummawa.
A can gida kuma, sabuwar gwamnatin jihar ta Filato da ta soma aiki a watan Mayun da ya gabata, ta ce ta samo bakin zaren warware matsalar tashe-tashen hankula a jihar.
A can baya dai Filato jiha ce da a kullum take cike da baki ‘yan kasashen waje musamman turawa saboda kyakkyawan yanayi da zaman lafiya. To sai dai hakan ya kau a ‘yan shekarun baya-bayan nan sakamakon tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Wannan shi ne babban abin da ya dami akasarin ‘yan jihar da ke zaune a Amurka.
Saurari cikakken rahoto daga Murtala Faruk Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5