Wata kungiya mai suna Center Obota ce ta shirya wannan taro a ci gaba da neman hanyoyin karfafa zaman lafiya da mahimmanci yafiya a addinance.
A shekarar 2015 rikicin ya barke a Jamhuriyar Nijar wanda aka danganta da rikicin batanci da ya auku na Cherlie Hebdo a kasar Faransa.
“Ya kamata Malamai su rika horar da mabiyansu kan ma’anar addini, ya kuma kamata ‘yan siyasa kada su rika taba addini” In ji Salihuo Jeka, jami’i a kungiyar ta Obota yayin da yake bayani kan muhimmancin taron.
Da yawa daga cikin mahalarta wannan taro, sun yaba da shirin wanda suka ce zai kara dankon zumunci tsakanin mabiya addinan biyu.
“Wannan taro yana da muhimmanci a gare mu mu da muka zo da yaranmu da tunda kwanciyar hankali a cikin kasa abu ne mai muhimmanci.”In ji Malama Usaina Samir wata mai bin addini Kirista da ta halarci taron.
A shekarar 2015 wata zanga zangar nuna kyama ga kamfanin mujallar Cherlie Hebdo wacce ake bugawa a Faransa bayan da ta yi batanci ga Annabi Muhammad tsira da amince Allah su tabbata a gare shi, ta barke a Jamhuriyar ta Nijar.
Boren ya kai ga wasu bata gari suka afkawa wasu mujami’u dake Jamhuriyar Nijar lamarin da aka yi tir da shi a duk fadin duniya.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin cikakken rahoto kan taron da Cibiyar Otoba ta shirya:
Your browser doesn’t support HTML5