An Gudanar Da Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar

Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar matan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula, da na addinai sun gudanar da taron addu’o'in zaman lafiya mako guda bayan da ‘yan ta’adda suka halaka sojojin kasar 71 a barikin soji da ke Inates a kusa da kan iyakar kasar da Mali.

Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar

An kaddamar da shirin ne a dakin taro na "Academie des Arts Martiaux" da ke birnin Yamai, inda mata kimanin 1500 suka hallara domin yi wa jami’an tsaron Nijar addu’o'i a yakin da suke ke yi da ‘yan ta’adda.

Kungiyoyin fararen hula da na addinai, da jam’iyun siyasa ne suka shirya wannan taro da nufin karfafawa dakarun tsaro kwarin guiwa.

Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar

Mata daga bangarorin siyasa daban-daban sun halarci wannan taro da nufin gwadawa jama’a cewa sha’anin tsaro magana ce da ta shafi dukkan ‘yan kasa.

Harin ta’addancin da ya hallaka sojoji sama da 70 a makon jiya na ci gaba da bakanta wa jama’a a rai, inda yanzu haka shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da aika wa shugaba Issouhou Mahamadou da sakonnin ta’aziya.

Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar

Kuma rahotanni na nuna cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, zai ziyarci Nijar ranar Lahadi mai zuwa, domin jajantawa jama’a game da wannan babban rashi, duk da cewa wasu ‘yan Nijar na zargin Faransa da hannu a kashe-kashen da ake fuskanta a yankin Sahel.

A saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Taron Addu’o'in Zaman Lafiya A Jamhuriyar Nijar