Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, da Faraminista Matteo Renzi da kuma manyan wakilan Paparoma Francis, suna daga cikin daruruwan masu makoki da suka halarci jana’izar da aka yi cikin ruwan sama.
Da farkon addu’oin jana’izar, Bishop Demonico Pompili ya karanta sunayen mutanen dari biyu da arba’in da biyu da suka mutu a garin Amatrice da kuma Accumoli.
Ya yi amfani da wannan damar wajen tsautawa kan rashin ingancin ginin da ake zaton ya yi tasiri a yawan mutanen da suka rasu. Yace girgizar kasa bata kisa. Abinda yafi kisa shine aikin mutum.
Yace tilas ne a sake gina yankin, domin kin yin haka sai sake kashe su karo na biyu. Sai dai ya yi gargadi da cewa kada a fake da sake gina yankin wajen wawushe arzikin kasar.
Kasar Italiya tayi kaurin suna a fannin miyagun ayyuka da kuma kazamin kudin da ake laftawa kwangilar ginin gwamnati, musamman gine ginen da ake yi bayan bala’oi. Masu bincike sun kaddamar da bincike kan girgizar kasar da ta auku ranar ishirin da hudu ga watan Agusta inda gine gine da dama suka rushe duk yake an yi masu gyaran fuska da kudin al’umma.