Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Hallaka Mutane 20 A Somalia


Baraguzan motar da aka kai harin kunar bakin wake da ita
Baraguzan motar da aka kai harin kunar bakin wake da ita

Wani bam da ya fashe a cikin wata mota kusa da fadar shugaban kasar Somalia a babban birnin kasar Mogadishu ya kashe mutane akalla 20 kuma ya jikata sama da mutune 30 a cewar jami’an tsaro.

Jami’an tsaron fadar shubagaban sun shaidawa Muryar Amurka sukace wata mota mai tsananin gudu ne ta nufosu. Sun yi harbin gargadi cikin iska, amma sai motar taki tsayawa nan ne suka bude wuta akan motar sai bam din ya fashe.

Motar tayi karo da bangon wani gidan otal da ake kira SYL Hotel wanda yake kusa da ginin fadar shugaban kasar wato Somalia Villa.

Ministocin kasar guda biyu suka samu raunuka da wakilan majalisa su biyu da kuma yan jarida guda biyu wadanda suke cikin otal a lokacin da fashewar ya auku.

Kungiyar Al-Shabab ta saba kai irin wa’yannan hare-hare a gidajen otal a nan Mogadishu saboda nan ne jam’an gwamnati suka saba yin tarukansu. Al-Shabab ta taba kai hari a nan Otal SYL a cikin watan Faburairu , harin da yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane tara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG