Nijar: An Cika Shekaru 24 Da Samar Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya

A yayin da ake shagulgulan tunawa da zagayowar ranar cika shekaru 24, da kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan tawayen Arewacin Jamhuriyar Nijar da gwamnati, wani tsohon kwamandan kungiyoyin 'yan tawayen ya nuna damuwa a game da yadda ake jan kafa wajen zartar da wasu daga cikin shawarwarin da aka tsayar a shekarar 1995.

A shekarar 1991 ne abzinawan yankin Ayeri suka dauki makamai da nufin kwatantawa hukumomin Nijar bacin ransu, akan rashin basu damar shiga a dama al’amuran kasa da su, alhali akasarin albarkatun karkashin kasar Nijar na yankin su ne, sai dai bayan fadace-fadace na tsawon shekaru 3, bangarorin 2 sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 24 ga watan Afrilun 1995, mafarin tsayar da wannan rana a matsayin ta hadin kan ‘yan kasa.

A yayin da hukumomin da jama’ar kasa ke murnar zagayowar wannan ranar, tsofafin ‘yan tawayen ana su bangare na korafi a game da abin da suka kira jan kafar dake tattare da shirin zartar da alkawutan da aka dauka yau shekaru 24 cif.

Domin jaddada mahimmancin wannan rana ta 24 ga watan Afrilu a gareta gwamnatin Nijar ta shirya bikin musamman, dake gudana a yau Laraba, tawagogi daga sassan kasar sun halarci taron na jaddada zaman lafiya.

Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Bukin Zagayowar Zaman Lafiya A Nijar 2'30"