An Kashe akalla mutum 11 a harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai wa ayarin motocin jami’an tsaron gwamnan da mutanen da ake maida su gidajen su a garin Baga a cewar majiyoyin ‘yan sanda da jami’an tsaro.
Ayayrin motocin gwamnan ya na kan hanyar sa ne ta komawa da mutanen garin Baga da ayyukan Boko Haram ya sa suka yi kaura daga gidajen su domin fara wani shiri da hukumomin jihar Borno suka bullo da shi. Jihar Borno dai ta sha fama da boren ‘yan ta’adda a baya.
A cikin watan Yulin wannan shekara ma, Gwamna Zulum ya fuskancin irin wannan hari na kungiyar ‘yan ta’adda a wajen garin Baga, lamarin da ya tilasta masa soke bulaguron na shi zuwa cikin garin.
Duk da cewa an kashe jami’an tsaron fiye da goma da kuma jikkata fararen hula, amma hakan bai hana gwamnan ci gaba da yunkurin sa ba na shiga garin Bagar, sai dai wasu masu lura da al’amura suna ganin ya kamata gwamnan ya hakura ya maida komai ga Allah, ganin irin rayuka da ke salwanta a kan wannan hanya.
Masu fashin baki sun ce har yanzu hanyar Baga bata da kyau kuma ana asarar rayuka, don haka "kada gwamnan ya yi aiki da fushin zuciya, ya nemi shawarwarin masana a kan wannan lamari kafin ya sake wani yunkuri na maida ‘yan gudun hijira gidajen su."
Manazarta na ganin harin na ranar Juma’a a zaman wani babban mummunar al’amari da ya faru a cikin tawagar gwamnan, ganin cewa an yi asarar rayuka da dama musamman na jami’an tsaro da kan bada kariya ga al’umma.
Daga Maiduguri ga Rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5