A ranar Juma’a ofishin jakadancin Amurka a kasar Mozambique ya gabatar da kashedi akan tsaro yana yiwa Amerikawa gargadin su gujewa kai ziyara gundumar Palma dake lardin Cabor Delgado, wadanda suke can kuma, su yi nazarin ficewa daga yankin nan take.
Ofishin jakadancin ya gabatar da wannan kashedin ne a saboda bayanai daya samu na yiwuwar kaiwa cibiyoyin gwamnati da wasu cibiyoyin hare hare a yankin.
Cikin makoni biyu da suka shige wasu yan yakin sa kai sun kai munanan hare hare da ‘yan sanda suka danganta da wata kungiyar Musulmi dake arewacin kasar.
A hare hare na baya bayan nan da aka dora laifin su akan wata kungiya da ake kira Mozambique Al Shabab, yan yakin sa kai dauke da wukake da ada sun kashe mutane biyar a gundumar Quissanga a daren shidda ga wannan wata na Yuni.
Kwana daya kafin aukuwar wannan al’amari mutane bakwai aka sassare har lahira a gundumar Macomia yayinda kuma aka kona fiye da gidaje dubu daya.