Masu bincike sun gano wata kafa a manhajar kamfanin Apple da zata iya baiwa masu kutse damar shiga na’urorin mutane musamman kwamfutar Mac da wayar iphone ta hanyar aikawa da sakonnin kar ta kwana.
Wani mai bincike daga Cisco Talos kamfanin tsaro a fannin fasaha shine ya gano cewar masu kutsen kan iya aikawa da fayil na hoto da ake kira .TIF wanda shine zai baiwa masu kutsen damar samun bayanin sirri dake cikin na’urar.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa, Tyler Bohan daga kamfanin Cisco Talos yace, “irin wannan kofofi abin damuwa ne domin za a iya samunsu a manhajojin da ke a na’urar Apple.
Ya kuma kara da cewa “ya danganta da hanyar da mai kutsen ya zaba, irin wadannan gurbatattun hanyoyi basa bukatar sai mai kutsen ya yi mu’amula da mai na’urar kafin ya samu hanya, tun da irin ire-iren mahajoji kamar su iMassage na sarrafa hotunan da suka karba da kansu.
An dai samu wannan matsala ne kan wasu na’urorin da ke amfani da manhajar Apple ta iOS da ta OS X, amma duk masu amfani da kayan Apple wanda ke sabunta manhajarsu ta yin update ba zasu sami wannan matsala ba.
Your browser doesn’t support HTML5