A karamar hukumar Chanchaga mai hekwata a birnin Minna fadar gwamnatin jihar Neja, shugaban karamar Yusuf Fuka yace binciken da suka gudanar a fannin makarantun firamari ya sa an gano makarantun firamari 22 na bogi.
Karamar hukumar ta share shekaru goma cur tana biyan albashin malamansu alhali kuwa babu makarantun a karamar hukumar.
Onarebul Yusuf Fuka ya yi karin bayani kan lamarin. Yace duka duka makarantun firamarin da karamar hukumar take dasu 32 ne. Yace amma a duk lokacin da suka zo bincike sai su ga wasu da basa cikin lissafinsu. Yace akwai irin wadannan makarantun 22 da karamar hukumar take biyan albashinsu amma kuma basa cikin karamar hukumar.
Karamar hukumar ta dauki matakin dakatar da sakatariyar sashen ilimi Dr. Ramatu Haruna da wasu manyan jami'an karamar hukumar su biyu domin cigaba da gudanar da bincike a fannin ilimi.
Shugaban hukumar bada ilimi na bai daya na jihar Alhaji Alhassan Bawaniworo yace karamar hukumar bata da ikon dakatar da sakatariyar ilimin karamar hukumar. Yace duk ma'akacin da albashinsa ya kama daga mataki na bakwai karamar hukuma bata iya dakatar dashi daga aiki saidai a matakin jiha.Kamata yayi karamar hukumar ta aiakawa jiha abun da ta gano.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5