An Gano Ma’adinnan Karkashin Kasa Fiye Da Talatin Da Za Su Iya Sauya Rayuwar Mutane A Najeriya

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta gano ma’adinan karkashin kasa fiye da talatin a Jihar, da take da yakinin sarrafasu zai janyo ingantan tattalin arziki da kawo saukin masifun rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

NASARAWA, NIGERIA - Jihar Nasarawa dake tsakiyar Najeriya, ana mata kirari ne da ‘’Gidan Ma’adinai’’, saboda irin nau’i’kan ma’adinai da ke dankare a karkashin kasarta da gwamnatocin baya suka yi rikon sakainar kashi wa bangaren.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce a yanzu haka sun samo kampanoni manya da zasu zuba jari a bangaren ma’adinan don bunkasa su da farfado da wassu hanyoyin samarda arziki a kasar.

Ku Duba Wannan Ma Ra’ayoyi Mabanbanta Kan Haramta Hakar Ma’adinai a Zamfara

Yawancin wuraren da ake samun ma’adinai a Najeriya, akan sami rikice-rikice, abinda gwamnan ya ce suna bin matakan da suka dace don hana tashin hankali.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana sane da albarkatun kasa fiye da arba’in da hudu da suka hada da karafa, gwal, duwatsu masu daraja, kwal da sauransu, da ake amfani dasu a masana’antu da sarrafa makamashi da zasu iya sauya rayuwar mutane fiya da miliyan dari biyu a kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

An Gano Ma’adinnan Karkashin Kasa Fiye Da Talatin Da Za Su Iya Sauya Rayuwar Mutane A Najeriya