Kasidun tamkar yin nazari ne akan halin da Najeriya ke ciki.
Shaikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin wadanda suka gabatar da kasidu. Taken kasidar da ya gudanar ita ce "Wa zaka zaba"
Shaikh Gumi yace kowa abun da yake so a Najeriya shi ne zaman lafiya. Sai an sami zaman lafiya za'a iya tunanin wasu abu nan gaba. Amma kuma ba'a samun zaman lafiya sai an zabi mutumin da duk bangaren kasar sun amince dashi.
Shaikh yace idan ana maganar daula shekaru 54 shekaru ne 'yan kadan domin wasu dauloli sukan yi shekaru dubu. Sabo da haka kasar tana nan tana rarrafe. Abun da ya faru yanzu kamar wani bakin hadari ne yake wuce wa a gari. Abun da yakamata a yi a hada kai a zabi wanda zai kawo zaman lafiya.
Hajiya Hafsat Muhammed Baba ta gabatar da kasida mai taken "Arewa ina muka dosa" Tace yakamata 'yan arewa su hada kansu su kuma san inda suka fito da kuma inda suka nufa. 'Yan arewa su tabbatar cewa yadda kudu ta fitar da mutum daya to arewa ma tayi hakan. Kwadayi yasa 'yan arewa sun lalace. Sauran kasar na ganin 'yan arewa kamar kaska mai shan jini.
Shehu Sani cewa duk da shekarun da Najeriya ta kwashe har yanzu tana fama da rashin shuwagabanni masu adalci. Sarakuna da masu mulki da masu hannu da shuni sun wawure arzikin kasar sun bar talaka bashi da komi sai wahalar da yara da lebura da marasa galifu suke fama da ita cikin shekaru 54. Rashin gaskiya da rashin adalci sun yiwa kasar katutu.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5