Daya daga cikin manyan labarai masu daukar hankali a cikin shekaru biyu na shugabancin Donald Trump za su fita fili tare da fitar da rahoton binciken kwamiti, na musamman na Robert Mueller, game da zargin shishshigi da karya doka a zaben shugaban Amurka.
Babban Atoni Janar, William Barr, yana shirin yin bayanai game da rahoton Mueller, a yau Alhamis, jim kadan bayan ya turawa Majalisa bayanan sannan kuma daga bisani za’a saka shi a yanar gizo.
Karo na farko, Majalisa da jama'ar Amurka za su gani da kansu abin da Mueller ya binciko yayin da shi da masu taya shi binciken suke kokarin sanin ko ma su yi wa shugaba Trump ya’kin neman zaben sa, na da hannu a ‘katsalandan din da Rasha tayi, a zaben shekarar 2016, wanda Trump ya lashe.
A farkon shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, hukumomin leken asirin Amurka, sun ha’kikanta cewa Rasha bisa umarnin shugaban kasar, Vladimir Putin,sun yi shishshigi a yakin neman zaben Amurka tare kuma da nuna fifiko ga nasarar shugaba Trump.