An Fidda Bayanai Kan Dan Bindigar Da Ya Kashe Mutum 12 a Virginia

Lokacin da 'yan sanda suka mamaye wurin da aka kai harin na virginia a, Amurka Mayu 31, 2019.

Shugaban ‘yan sandan yankin, James Cervera keya ce, “dan bindigar ya shiga cikin ginin ne, dauke da bindigar hannu nau’in da ake kira Calibre 45.” Ya kuma harbe mutanen.

‘Yan sanda a jihar Virginia da ke nan Amurka, sun bayyana sunan dan bindigar nan da ya harbe mutum 12 har lahira a matsayin Dewayne Craddock mai shekaru 40 da haihuwa, sun kuma ce daga wannan lokaci da suka bayyana sunan nasa, ba za su sake ambatarsa ba.

Rahotanni sun bayyana dan bindigar a matsayin ma’aikaci a wata ma'aikata ta gwamnati, wanda ya kai harin yana mai cike da fushi.

Ya kuma harbe mutun 12 ne a yankin Virginia Beach da ke bakin teku, inda shi ma daga baya ‘yan sanda suka harbe shi.

Shugaban ‘yan sandan yankin, James Cervera keya ce, “dan bindigar ya shiga cikin ginin ne, dauke da bindigar hannu nau’in da ake kira Calibre 45. Ya kuma harbe mutanen.

Shugaban ‘yan sanda ya kwatanta dan bindigar a matsayin ma’aikaci da aka batawa rai.

Sai dai bai yi wani karin bayani ba kan wannan hari, amma ya ce yanzu haka ana akan bincike, duk da cewa sun fahimci shi kadai ya kitsa wannan hari.