'Yan takara a zaben shugaban kasar da aka sha jinkirtawa a kasar Ivory Coast, sun fara yakin neman zabe gadan-gadan yau Jumma'a domin wannan zaben da a yanzu aka ce za a gudanar da shi ranar 31 ga watan nan na Oktoba.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar dake Afirka ta Yamma, Y. J. Choi, yayi rokon da a yi yakin neman zabe cikin lumana, ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa al'ummar Ivory Coast ba za su yarda tashin hankali ya sukurkuta musu wannan zabe ba.
An shirya zaben mai zuwa da nufin sake hada kasar Ivory Coast a bayan yakin basasar 2002 wanda ya raba kasar gida biyu a tsakanin yankin Arewaci dake hannun 'yan tawaye da kuma Kudanci dake hannun gwamnati. Sassan biyu sun kafa gwamnatin hadin kan kasa a bayan wata yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2007.
An kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar domin tabbatar da bind oka da oda. Da ma dai sojojin majalisar sun kai dubu 8 da dari shida a kasar.