Babban sakataren hukumar 'yan sandan duniya, ta INTERPOL, ya yi karin bayani jim kadan bayan da aka bude taron kasa da kasa akan yaki da safarar mutane na yini biyu a Abuja babban birnin Nigeria.
A cewarsa taron ya tattaro baki daya masu ruwa da tsaki akan yaki da safarar mutane daga sassan duniya daban daban. Akwai kimanin wakilai 500 da za su tattauna akan wannan muguwar sana'ar cikin yini biyu.
Ana taron ne da zummar dakile harkokin masu satar mutane da neman yadda za'a ragargaza masu tafka miyagun laifuffuka, cin hanci da rashawa, da kuma ceto wadanda bala'in satar mutane ya rutsa dasu. Sakataren ya ce za su tsara yadda za su tunkari duk wadannan matsalolin.
Babbar daraktar hukumar yaki da fataucin mutane ta Nigeria ta ce hukumarsu na hada kai da hukumar 'yan sanda ta duniya wato INTERPOL tun shekarun baya. Ta ci gaba da cewa albarkacin dangantakar dake tsakaninsu da hukumar ya sa Nigeria ta samu damar daukar nauyin taron. Wannan kuma shi ne karo na farko da hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa za ta shirya wani taronta a nahiyar Afirka, musamman a Nigeria. Ta ce suna fatan ci gaba da aiki da juna cikin hadin kai da fahimtar juna.
A saurarin karin bayani a wannan rahoton na Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5