Sanata Abu Ibrahim shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da harkokin 'yansanda a firar da yayi da Muryar Amurka ya bayyana matakan da aka shirya na daukan 'yansandan da ake bukata ba tare da barin addini, kabilanci ko bangaranci sun dagula shirin ba.
Sanata Abu Ibrahim yana wakiltar Katsina ta kudu. Yace wadanda suka nemi shiga aikin 'yansanda sun kai wajen dubu dari takwas amma an yi anfani da naura mai kwakwalwa kuma an gaya mata irin ma'aikatan da ake bukata. Duk wanda bai bi ka'ida ba naurar ta cireshi.
Yace jama'a su lura cewa an bi ka'idodi. Babu rashin gaskiya a lamarin. Babu maganar siyasa ko kabilanci ko addini. Duk kananan hukumomi dari bakwai da saba'in da hudu zasu samu nasu. Kowacce karamar hukuma za'a dauki dansanda kurata tara. Haka ma kowace jiha zata samu sifeto 12 da masu mukamin ASP 12.
Mataki na gaba zai kaiga komawa jiha jiha inda za'a tantance wadanda suka fito daga jiha. Daga nan kuma sai a je kananan hukumomi inda za'a yi tantancewar karshe.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5