Yadda Aka Fara Aikin Shigar Da Kayan Agaji Cikin Gaza

Ayarin dogayen motocin da ke shiga da kayan agajin zuwa Gaza

Dozin-dozin din dogayen motoci sun kwashe kwanaki a kusa da Rafah suna dakon a bude bodar don shigar da kayayyakin agaji cikin Gaza mai mutum sama da miliyan biyu.

Wani ayarin dogayen motoci 20 daga kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Masar dauke da kayayykin agaji ya fara shiga yankin Zirin Gaza a ranar Asabar.

Kayayyakin wadanda aka shiga da su ta iyakar yankin Rafah da Masar ke kula da ita, sun hada da abinci, magunguna da kuma ruwa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna godiyarsa ga hukumomin Masar kan rawar da suka taka wajen shigar da wadannan kayayyaki.

Sai dai ya ce al’umar yankin Gazan na bukatar sama da wannan adadin kayayyakin da aka fara shigarwa, yana mai cewa Majalisar Dinkin Duniyar na aiki da dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin wajen ganin an samu damar shigar da karin wasu kayayyakin.

Dozin-dozin din dogayen motoci sun kwashe kwanaki a kusa da Rafah suna dakon a bude bodar don shigar da kayayyakin agaji cikin Gaza mai mutum sama da miliyan biyu.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce wannan dama da aka samu ta shigar da kayayyakin agaji ta biyo bayan tattaunawar diflomasiyya da Amurka ta yi ta yi ne da shugabanni a yankin.

Yayin wani taron koli da aka yi a birnin Al Qahira na kasar Masar, Kasashen Masar da Jordan sun soki Isra’ila kan hare-haren da take kai wa a yankin Gaza.

Masu lura da al’mura na ganin kalaman kasashen biyu wadanda suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila gomman shekaru da suka gabata, kuma suka kasance kawaye ga kasashen yammacin, wata alama ce da ke nuna cewa sun fara gajiya da yakin Isra’ilan ta kaddamar da Hamas wanda aka kwashe makonni biyu ana yi.

Shugaban Masar Abdel Fatah El Sisi, wanda ya jgoranci taron, ya yi fatali da duk wani batu da ya shafi korar al’umar Gaza mai yawan mutum miliyan 2.3 zuwa yankin Sinai, yana mai gargadi ga “duk wani yunkuri na murkushe fafutukar Falasdinawa.”

Sarkin Jordan Abdullah na Biyu, ana shi bangaren ya ce kawanya da bama-baman da Isra’ila take ta harba wa cikin Gaza sun zama “laifukan yaki.

Ita dai Isra’ila ta ce sai ta ga bayan mayakan Hamas da shugabanninta amma ba kasafai take magana kan lokacin da za ta kawo karshen yakin ba.

A ranar Juma’a Ministan tsaron kasar Isra’ila Yoav Gallant, ya bayyana wani jadawali mai dauke da fannoni uku, wanda ya shata yadda kasar ta Isra’ila za ta kai hare-haren sama da kara kusantar yankin na Gaza – wani abu da ke nuni da kutsa kai da dakarun kasar za su yi don kawar da Hamas.