An Fara Samun Matsalar Wutar Lantarki A Jamhuriyar Nijer

Kayayyakin Samar Da Wutar Lantarki

Mazauna yankunan Yamai da Dosso da Tilabery sun fada cikin mawuyacin halin rayuwa a sakamakon daukewar wutar lantarki da ake huskanta yau kimanin kwanaki uku, matsalar da kamfanin wutar lantarki Nigelec ya danganta da faduwar wasu karafunan tangarafu tsakanin birnin Kebbi da birnin Gaure.

Karar injin jenerato ta mamaye galibin manyan titunan birnin Yamai daya daga cikin biranen da suka fada cikin matsalar wutar lantarki a ‘yan kwanakin nan inda a wasu unguwannin ake shafe tsawon wuni ko tsawon dare ba tare da samun wutar lantarki ba a wani lokacin da ake fama da matsanancin yanayin zafi.

Dama tun farkon watan wannan watan Mayu ne darektan kamfanin Nigelec Khalid Alassan ya sanar da al’umar Nijer cewa lalacewar injin kamfanin na tashar Goudel a watan Nuwamban da ya gabata na daga cikin dalilin da suka haddasa karancin wutar lantarki.

Darektan kanfanin ya kuma nuna damuwarsa ganin cewa a wannan Azumin watan Ramadan lokaci ne na tsananin zafi da aka fi yawan amfani da wuta sosai a yayin da daya daga cikin injinan tashar Gorou sun daina aiki a wani lokacin da ake kara samun yawaitar mabukatan wutar lantarki.

Matsalar wutar lantarki wata dadediyar magana ce da kusan ta kan tasowa a kowace shekara idan yanayin zafi ya zagayo abin da ya sa gwamnatin Nijer soma hangen kafa tashoshin samar da wutar lantarki da hasken rana.

Sule Mumuni Barma daga birnin Yamai nada karin bayani a wannan rahoto:

Your browser doesn’t support HTML5

MATSALAR WUTA A NIJER