An Fara Sakawa Karnuka Kyamara Don Inganta Tsaro A Amurka

Jihohin Oregon da Wisconsin na Amurka sun fara amfani da wasu kyamarori da ake makalasu a jikin karnukan ‘yan sanda da ake kira K-9.

Ita dai kyamarar za ta taimaka wajen ganin irin halin da karen da ke dauke da ita yake ciki, a lokacin da yaje kamamai laifi.

A cewar jami’n hukumar, wannan kyamarar za ta taimaka a duk lokacin da aka tura kare ya shiga cikin mutun ko kuma aka sake shi cikin daji don kamo wanda ake nema, ko kuma a duk lokacin da ya shiga cikin daji wajen neman mutum ko wasu abubuwa da aka umurce shi da ya nemo.

Akan yi amfani da wadannan karnukan wajen gano wasu abubuwa da aka haramta amfani da su, kamar kyanwa, ko kanshin jikin mutum, duk a lokacin da karen ya shiga wuri idan akwai wani abu da aka koya mishi ganowa zai shaida ma shugaban shi cewar akwai wani abu da bai kamata a ce yana wajen ba.

Ku Duba Wannan Ma China Ta Kirkiro Na'ura Mai Gane Mutum Daga Tafiyarsa

A duk lokacin da kare ya shiga wani wuri, kyamarar za ta dinga nunama shugabansa halin da yake ciki, da masaniyar irin shirin da suke bukata wajen tunkari inda yake, koda mai laifi na rike da wani makami za’a iya gani ta kyamarar.

Hakan zai taimaka wajen rage yadda masu laifi ke kai ma jami’an ‘yan sanda hari lokacin aikin su, kana zai ba da damar a ga halin da shi ma karen yake don ba shi taimakon gaggawa.

An kiyasta kudin kyamarar da yake kai wa dalar Amurka $10,000 kwatankwacin Naira milliyan 3.6.