Miliyoyin Amurkawa ne zasu fita don kada kuri’ar su gobe idan Allah ya kai rai, wanda zasu zabi ‘yan majalisun dattawar kasar, da wadansu gwmanoni a daukacin kasar.
Cikin ‘yan watannin da suka gabata ne kamfanin zumunta na Facebook ya fuskanci matsanciyar bincike, da ake zargin kamfani da bada kafofin yada labarai da basu da tushe.
Kana wasu mutane kanyi amfani da shafufukan karya don yada wasu manufofinsu, haka mutane da dama kanyi amfani da shafin wajen bayyanar da ra’ayoyin su da kuma cin zarafin wasu.
Daya daga cikin ma’aikatan kamfanin na Facebook Peter Sterm, ya jaddada manufofin kamfanin nasu, da cewar an kirkiri kamfanin ne da zummar samar da hanyoyin sadar da zumunta cikin sauki.
Da bada damammaki ga mutane a fadin duniya don bayyanar da ra’ayoinsu wajen hadin kan jama’a. Ya kara da cewar bukatar su shine, mutane su dinga shiga shafin na Facebook batare wani shakkaba.
Hakan ma yasa kamfanin daukar ma’aikata 20,000 da kawai zasu dinga duba labnaran da aka saka a shafin da suke nuni da cin zarafin wasu, ko kuma batanci da yada wasu labarai da basu da tushe.
Facebook Forum