An Fara Nazarin Sauya Tsarin Aikin 'Yan Sanda A Amurka

  • Ibrahim Garba

Wasu 'Yan Sand A Amurka

‘Yan Majalisar Dokokin Tarayyar Amurka na nazarin wasu shawarwari na sauye sauyen tsarin aikin ‘yan sanda a kasar, a yayin da jami’an gwamnati a matakan jahohi da kananan hukumomi, ke ta shelar daukar karin matakai na rage kudaden da su ke kashewa kan ‘yan sanda, da kuma rage masu izinin amfani da karfi.

Yau Laraba Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Harkokin Shari’a zai saurari ba’hasi daga wurin Philonise Floyd, dan’uwan George Floyd, ba Amurke bakar fatar nan da mutuwarsa a hannun ‘yan sanda, sanadiyyar danne masa wuya da wani dan sanda ya yi na tsawon kusan minti 9, ta janyo zanga-zanga a fadin kasar ta neman sauyi.

Sauran wadanda za su ba da ba’hasi sun hada da babban jami’in ‘yan sanda na Houston, Art Acevedo da kuma tsohuwar shugabar sashin kare hakkin dan adam na Ma’aikatar Shari’a kuma a yanzu shugabar kungiyar Kare ‘yancin ‘yan kasa, Vanita Gupta.