Ranar Talata 24 ga watan Nuwamba ne gwamnatin Nijer ta fadi cewa Tandja ya rasu a Yamai babban birnin kasar, amma takamaimai ba ta bayyana dalilin mutuwarsa ba.
An zabi Tandja a matsayin shugaban kasa har sau biyu a Nijer daga shekarar 1999 zuwa 2010 kafin aka yi mashi juyin mulki saboda ya yi yunkurin yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul, don ya samu damar ci gaba da mulki.
Hambarar da gwamnatin Tandja ne ya ba Issoufou Mahamadou damar zama shugaban kasa a zaben shekarar 2011 da aka yi. Mutuwar Tandja dai na zuwa ne kasa da wata daya kafin zaben shugaban kasar Nijer.
Tandja, wanda ya rasu ya na da shekara 82 a duniya, ranar Alhamis 26 ga watan nan shugaba Issouhou Mahamadou zai jagoranci wani taro na karrama shi da za a yi kafin a yi jana'izarsa a garinsa na asali wato Maine Soroa da ke jihar Diffa.
Wani dan majalisar dokokin Nijer, Lamido Moumouni Harouna, ya shaida wa Muryar Amurka cewa marigayi Tandja Mamadou dan kasa ne na gari wanda ya yi ayyukan kyautata rayuwa a karkara da yawa, tabbas Nijer ta yi babban rashi.
Saurari cikakkiyar hirar Lamido da Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5