A yau ne kasashe suka fara kece raini a fagen kwallon kafa a kasar Rasha inda ake soma gasar cin kofin duniya na wannan shekarar, inda kuma ita mai masaukin (Rasha) zata soma da gwabzawa da Saudi Arabia a wasar farko ta gasar.
WASHINGTON D.C —
Shugaban Rasha Vladimir Putin zai kasance daya daga cikin dubban mutanen da zasu halarci bude wassanin a filin wasa na Luzhinki (Lujinki) dake Moscow, mai daukar mutane sama da dubu 80.
Rasha za ta kashe zunzurutun Dala milyan dubu 13 na Amurka wajen daukar nauyin gasar, kuma an baza wassanin zuwa birane 11 na Rasha.
Za a gudanar da Gasar Cin Kofin Duniyar ne daga yau har zuwa ran 15 ga watan gobe na Yuli.
Wasu daga cikin kasashen da ake jin za su iya cin kofin sun hada da Brazil, Faransa, Spain, Argentina da kuma Jamus wacce ita ke rike da kofin a yanzu.