An Fara Karancin Kayan Masarufi A Kasuwannin Amurka

Layin kayan gwangwani

Ya zuwa yanzu mutum 41 ne aka samu dauke da cutar Coronavirus, a jihar Pennsylvania ta Amurka.

Gwamnan jihar Tom Wolf, ya bada sanarwar rufe makarantu tun daga matakin firamare har zuwa jami'a.

Za a gudanar da darusa ta kafofin yanar gizo kuma makarantun za su kasance rufe hara na tsawon makonni biyu.

Layin saida Shinkafa

Da safiyar yau Asabar 14 ga watan Maris, Muryar Amurka ta zagaya cikin jihar don ganema ido.

Shagon Walmart na daya daga cikin manyan shaguna da ke karamar hukumar Indiana a jihar Pennsylvania, kana kauyuka da suke zagaye da garin sukan je don siyayya.

Layin saida Taliya

Wadannan hotunan cikin shagon ne, inda za a ga cewar babu abubuwan more rayuwa da aka fi amfani da su, kamar shinkafa, wake, ruwan sha, takardar tishu, madara, kwai, da dai sauransu.

Mutane kuwa na ta cika shaguna a duk fadin Amurka domin siyan kayayakin da za su iya bukata, domin gudun ko ta kwana.

Hakan duk na faruwa yayin shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar saboda cutar ta Coronavirus.