Tun bayan da 'yan majalisun kasar Masar su ka amince da karin wa'adin shugaban kasar na ci gaba da zama a ofshinsa har zuwa 2030, yanzu haka al'ummar kasar da ke ciki da wajen kasar suma za su kada kuri'unsu kan lamarin.
WASHINGTON D.C. —
“Ku yi abinda ya kamata, ku kada kuri'ar amincewa," wasu daga sakonnin da alamomin da aka kafa jikin gidaje a fadin birnin al-Khahira ke dauke da su kenan. Babu wani bayyanannen adawa.
Irin tallata manufarsu da masu goyon bayan gwamanti su ka yi din na kiran da a yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulki don bai wa shugaban kasar Masar, Abdel Fattah el-Sissi, damar ci gaba da zama a ofishinsa har zuwa shekarar 2030.
Mutanan kasar Masar da su ke zaune a kasashen waje za su fara kada kuri’arsu a yau juma’a, kuma za a fara jefa kuri’a na kasa baki daya a gobe Asabar – kasa da sati daya bayan da ‘yan majalisa su ka amince da matakin.