An Fara Gwajin Maganin Rigakafin Cutar Ebola

Wata tana karbar allurar rigakafin cutar ebola a Liberia

Jiya aka fara gwajin maganin rigakafin cutar ebola a Liberia kasar da tafi wacce kamuwa da annobar cutar ebola

An fara wani gagarumin gwaji kan maganin rigakafin Ebola a Laberiya, a wani yunkurin kasashen duniya na hana sake fuskantar annobar da ta kashe mutane kusan dubu tara a yammacin Afirka.

An fara gwajin ne jiya Litinin a wani asibiti dake Monrovia babban binrin kasar, inda mutsane 600 suka amince su shiga jerin wadanda za'a gwada maganin akansu.

Gwajin, hadin gwiwa ne tsakanin Amurka da Laberiya.Magugunan da ake gwajin dasu suna kunshe da kwayoyin cutar Ebola da ba zai cutar ba,amma zai sa jikin mutum ya samu garkuwa. An tabbatar cewa magunguna biyu da wasu kamfanonin harhada magunguna da suke nan Amurka suka yi basu da illa ga Bil'adama a gwajin da za'a yi.

Masana daga Amurka da jami'an Amurka sun yi bayani ga manema labarai a Monrovia jiya Litinin, inda suka bada tabbacin cewa magungunan basu da wani illa.