An Fara Gasar Premier Ta Ukraine Yayin Da Ake Ci Gaba Da Yaki

Filin wasa na Olympiyskiy a birnin Kyiv, Ukraine, Fabrairu. 16, 2022.

Hukumomin kasar sun haramta taruwar mutane a wuri guda, gudun kada Rasha ta harbo maikaman roka, hakan ya sa aka hana 'yan kallo shiga filayen wasanni.

An bude gasar kwallon kafa ta Premier a Ukraine yayin da kasar ke ci gaba da gwabza yaki da Rasha.

A ranar Talata aka bude gasar ta 2022, amma an haramtwa masu kallo zuwa filayen wasanni.

Wasan farko an buga ne a filin wasa na Kyiv mai daukan mutum dubu 65 tsakanin Shaktar Donetsk da Metalist 1925, inda aka ta shi canjaras.

Kasar ta Ukraine na karkashin matakin soji na ko-ta-kwana, inda aka haramta taruwar jama’a a wuri guda, gudun kada Rasha ta harbo makaman roka.

Hakan na faruwa ne yayin da kasar ke shirin gudanar da bikin samun ‘yancin kai a ranar Laraba.

An ga ‘yan sanda a tsaye a bakin kofar shiga filin wasa, wanda ciyayi ya rufe wani sassanta sanadiyyar rufewa da aka yi watanni shida da suka gabata, amma babu dan kallo ko daya a cikin filin wasa.